Kakakin kungiyar tarayyar Turai ya byyana cewa Anreke Moro mataimakin babban sakataren kungiyar zai gana da Majid Takhtravanci, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran siyasa da wasu al-amura a birnin Geneva.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Perter Stonuo, yana fadar haka a jiya Litinin a birnin London, ya kuma kara da cewa a ranar Alhamis mai zuwa ne, wato 28 ga watan Nuwamba da muke ciki, Takht-Ravanci zai gana da jami’an kungiyar ta EU a birnin Geneva, sannan a ranar jumma’a kuma zai gana da jami’an gwamnatocin kasashen Burtania, Jamus da kuma Faransa.
Isma’ila Baqaee kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ya ce za’a gudanar da tattaunawar ne a matakin mataimakin ministan harkokin waje.
Kuma tattaunawar zata hada da al-amuran gabas tatsakiya musamman rikicin kasashen falasdinu da Lebanon.