A yau Alhamis ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ( ICC) ta fitar da samamcin a kamo mata Fira mininstan HKI Benjamin Netanyahu da kuma tsohon ministan yakinsa Yoav Gallant.
Bayanin da kotun manyan laifukan ta kasa da kasa ta fitar ya kunshi cewa, ba sai Isra’ila ta yarda da halarcin kotun ba, sammacin kamo shugabannin nata zai zama halartacce.
Kotun dai ta zargi Netenyahu da Gallant da aikata laifukan yaki da laifuka akan jinsin bil’adama da su ka hada da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.
Zargin da aka yi wa shugabannin HKI yana da alaka ne da yakin da har yanzu yake gudana akan al’ummar Gaza da kasashen duniya da dama su ke yin tir da shi.
A watannin baya ne dai Kasar Afirka ta kudu ta kai karar shugabannin HKI a kotun duniya, inda ta zarge su da aikata laifukan yaki akan al’ummar Falasdinu da ya hada da yi musu kisan kiyashi da kuma nuna musu wariya.
A farko-farkon yakin dai, Netenyahu ya nakalto littafin addinin Yahudawa na Talmud da ciki yake cewa a kashe abokan gaba, manya da kanana, mata da yara, da kuma dabbobinsu.
Shi kuwa ministan yaki Yoav Gallant ya bayyana Falasdinawa a matsayin dabbobi masu hatsari da za su dauki matakan da su ka dace a kansu.