223-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwashiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
////…. Madala, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan dan Fatima (s) diyar man manzon Allah(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda muke kawo maku sahabban manya All…(s) da kuma fitattun mutanen a lokacin suka fito suna bayyana damuwarsu da rashin amincewarsu da kissan da Mu’awiya dan Abusufyan yayiwa Hijru dan Adi da sahabbansa a lokacinda ya bukaci wamda asu zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) su kuma baranta kansu daga garashi amma suka ki amincewa.
Da farko mun ambaci Imam Al-Hassan (a) wanda ya rubuta wasika zuwa wajen Mu’awiya yana aibata shi kan mummunan aikinsa. Mun amabaci A’isha matar manzon All..(s) wacce mu’awiya ya shiga wajenta a gidanta a madina bayan ya dawo daga aikin hajji a wata shekara.
Sannan mun ambaci walin Mu’awiya a Kurasan, wanda ake kira Rabii dan Ziyad, wanda abin yayi masa zafi har ya yi yi kamar ya haukace. Ya aibata mutanen Kufa da farko da suka bari Ziyad ya kama Hijru dan Adi, da sahabbansa. Sannan bayan sun kashesu me yasa basu tawaye ba suka zauna shiru. Suka mika wuya ga sarakunan Banu Umayya suna yin abinda suka ga dama da mutane?. A nan, sai rana jumma’a ta zo ya yi sallar jumma’a tare da mutanen Khurasan. A cikin khudubobinsa sai ya ce wa mutane, ya gaji da rayuwa. Sannan ya ce masu zai yi addu’a, idan ya yi sai su ce Ameen.
Sai ya roki All..yana cewa idan yana ginan akwai sauran alkhairi tare da shi ya dauki rayuwarsa, sai All..ya amsa addu’ar ya kuma dauki rayuwarsa nan yake a wurin.
04-A yau zamu fara da Al-Hassan Al-bisri. Shi Hassanul Al-bisri sanennen Tabi’I ne, malami wanda a lokacin ya kasance mai rubutuwa Rabii dan Ziyad, walin Mu’awiya a Khurasan, wanda kuma muka kammala maganarsa.
An ruwaito daga Hassan Al-Bisri kan cewa, Kissan Hijru dan Adi yana daga cikin manya manyan laifuka guda 4 wadanda Mu’awiya dan abu sufyan ya aikata a lokzcin sarautarsa. Yana fada dangane da abinda ya shafi hijiru (halaka ta tabbata ga (Mu’awiya) kan Hijiru da mutanen Hijiru har sau uku ).
05-Abdullahi dan Umar. Wanda ya kidime a lokacinda aka bashi labarin kisan Hijru dan Adi da sahabbansa, an bashi labarin kissan ne a lokacinda yake cikin kasuwa, a zaune zaman harde kafafuwa (wata irin zama ) sai ya kwace zaman nasa ya tashi ya tafi yana kuka mai tsanani.
06-Mu’awiya dan Khudaij Al-Kindi. A lokacinda labara ya kai ga Mu’awiya dan Khudaij Al-Kindi, a lokacin yana yaki na fadada daular musulunci A Afirka, sai ya fadawa yan kabilar Kinda wadanda suke tare da shi, yana cewa: Kuna ganin, mu muna yaki wa kuraishawa muna kashe kammu ne kawai don mu karfafa mulkinsu ne, al-hali su kuma sun a can suna hawa kan yanuwammu suna kashe su”.
Ina son in tunatar da masu sauro kan cewa, wannan mu’awiya dan Khudaij shi ne ya kashe bawan Allah salihi, Mohammad dan Abubakar, gwamnan Imam Ali (a) a kan kasar Masar tare da umurnin Amru dan Asi. Da haka kuma ya share masa hanya ya zama gwamnan kasar Masar har ya mutu.
Don haka kashe Hijir dan Adi al-Kindi wani babban al-amari ne, kuma musiba ce, bala’ii ne, da ya faru a cikin tarihin musulunci, wanda ya girgiza musulmi, daga ciki har da sahabban manzon All..(s) da suka rage a lokacin. Hatta Mu’awiya kansa, ya fahinci cewa yayi barna, don haka an ruwaitoci sau da dama yakan ambci hijir a kebe da mutanensa sai ya ce : Musiba ta tabbata a gareni saboda kisanka ya Hijru. An ce a cikin rashin lafiyarsa ta karshe kafin Mutuwarsa, yakan cewa: Ranar da zan hadu don hisabi da Hijru rana ce mai tsawo. Ya fadeta har sau uku. Wato raar tana da wuya.
Ee, gaskiya ne, ranar da zai fuskanci hisabin Allah kan kissan Hijru babba ce, amma ba hijiru kadai ba, sai dai Hijiru da wasu masu kama da Hijru da dama, cikin salihan bayani masoya iyalan gidan manzon All..(s) da ya kashe. Ranakuna masu tsawon suna da yawa.
Bari mu ji kisser wasu yan uwan Hijiru wadanda, suma Mu’awiya yana da ranaku masu tsawo da su a ranar Kiyama. Na farkonsu da zamu kawo shi ne,
Rashidul Hijiri. Yana daga cikin musulmi masu tsentseni a addinindu, mai tsoron Allah, kuma malami mai falaloli da dama.
Rashid ya yi karatu a gaban Amirul muminina Aliyu dan Abi Talib (a), ya sha karatu da ilmi mai yawa a wajensa (a). Imam Ali (a) yana kiransa Rashidul Balaa, saboda sanin bala’in da zai same shi a bayansa.
Diyarsa mai suna –Qanu- tana cewa: Na ji babana (wato Rashidul Hijri yana cewa: Amirul muminina Aliyu dan Abitalib(a) ya ce mani: Ya Rashidu, wani irin hakuri zaka yi a lokacinda idan, shegen Banu’umayya ya kiraka, sai ya yanka hannayenka, da kafafuwanka, da kuma Harshenka?.
Sai nace: Ya Amural Muminina, amma karshen dai Aljanna ce?
Sai yace: Ya Rashidu kana tare da ni a duniya da Lahira. Wannan abinda diyarsa ta fada Kenan. Amma a wani hadisin kuma, Rashidul Hijri ko rashidul Balaa kamar yanda Amirul muminina (a) ya kira shi, yace wata rana ya fita tare da shi da Imam Ali (s) zuwa wani lambu, suka zauna karkashin wata bishiyar dabino, sai mai lambun ya tashi ya cire wani abu daga dabinon ya bawa imam Ali(a), sai muka ci, sai nace: Amma dabinon nan suna da dadi.?
Sai Imam(a) yace masa: Amma kai kuma da sannu za’a ratayaka a kashe ka kututturenta.
Don haka tun lokacin da ya ji wannan maganar daga wajen Imam Ali(a). Sai Rashidul Hijiri ya na zuwa wajen wannan dabinon da ya ci yayanta, ya bata ruwa ya shayar da ita. Sai ya bautawa All..a karkashinta. Ana cikin wannan halin sai wata rana ya zo ya ga cewa an sara samanta, sai kututturenta ne kawai ya rage, sai ya fahinci cewa ranar mutuwarsa ta kusa. Sai wata rana ya sake zuwa sai yaga an yanka rabin kututturen, ana kuma amfani shi wajen diban ruwa daga rijiya da shi. Sai ya kara yakinin cewa ajalinsaya kusa.
Ana cikin wannan mummunan halin a Kufa, sai Dan sumayya ya sa anemo shi. A lokacinda aka zo da shi. Sai yace masa: Menen abokinka (wato Imam Ali (a) ya fada maka yanda zamu da kai.
Sai Rashidul Hijiri ya ce: Ya ce mani zaku yayyanka hannu na da kafafuwa sannan ku tserene.
Sai dan Sumayya yace: Wallahi sai mun karyata maganarsa. Ku barshi ya tafi. Sai yansandarsa suka kyale Rashid ya kama hanyarsa yana tafi. Sai Ziyad y ace masu su je su dawo da shi. A lokacinda aka kawo shi sai yace: babu sami wani abu da ya dace da kai ba sai abinda abokinka (Imam Ali(a) ya fad aba. Don baka gushe ba kana aikata munana al-amura a garemu matukar kana raye. Ku yanka hannayensa da kafafuwansa. Sai yansandansa suka aikata umurninsa.
Suna yanka hannayen Rashid yana ta magana, sai maganarsa ta fusata Ziyad sai ya cewa yansadan ku tsereshi ku shake wuyarsa.
Sai Rashid ya ce: akwai abinda ya rage buku aikata a kaina ba, yana nufin yanke harshensa. Sai Ziyad yace a yanke harshensa. A lokacinda za’a yanke hershensa, sai yace ku bani lokaci dan kadan bari inyi magana, sai sukabashi. Sai Rashidul Hijiri, ko rashidul Bala’aa yace: wannan shi ne wallah! Gaskiyar labarin da Amirul muminina (a) ya fada mani na yanke harshen a. sai suka yanke harshensa.
Wani laifi ne wannan bawan All..yayi har ya kai ga suka cancanci wannan mummunan ukuba,? . sai dai gaskiyan al-amarin shi ne, Dan Sumayya da Mu’awiya suna son gamawa da dukkan wadanda suke son iylan gidan manzon All..(s) daga doron kasa. Suna son kawo karshen mazaharsu, wacce itace musuluncin da aka saukarwa manzon All..(s).
Sai kuma Amru dan Al-Hamkul Khuzaa’i. Ammu ya kasashen mutum ne mai riko da addini sosai, kuma yana daga cikin sahabban manzon All..(s), mai tsantsenine, mai tsoron All… Amru dan Al-Hamqul Khuza’i ne ya taba shayar da manzon All..(s) madara sai ya yi masa addu’ar Alkhairi. Ya rokamma masa All..ya tsawaita kurucciyarsa, wato ya dade yana matashi. Sai All..ya karbi addu’ar manzon All..(s), sai gashi Amru ya kusan 80 ba’a ga farin gashi a kansa ba.
Bayan manzon All..(s) ya kasance cikin zababbuna sahabban Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a). Kai yana daga cikin sahabbansa mafi kusa da shi. Imam Ali (a) yayi masa addu’a ya ce: {Ya Uabangiji ! Ka haskaka zuciyarsa da tsoron ka, da shiriya zuwa tafarki madaidaiciya} . Imam Ali (a) yana girmama shi, yana daukaka shi, yana gabatar da shi kan wasu da dama. Hakika wata rana ya fada masa cewa: