225-Asalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwashiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
////….Madala, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan dan Fatima (s) diyar man manzon Allah(s) da muke kawo maku, a cikin shirummu da ya gabata mun karasa magana dangane da da Amru dan Al-Hamkul Khuzaa’i, da abokinsa wanda ake kira Rafa’ah dan Shaddad, inda suka gudo daga Kufa suka koma Mada’in da farko saboda suna jin tsaron Mu’awiya zai sa a kamsu a kashe, musamman bayan ya tura Ziyad dan Sumayya a matsayin walinsa a Kufa. Bayan wani lokaci suka ji cewa Mada’in bai da amincin da ya dace, sai suka kama hanyar Musil. A lokacinda suka isa musil sai suka boye kansu a cikin wani kogo a bayan garin. Amma wasu mutane sun kansu a lokacinda suke shiga kogon don haka suka tsegintawa mahunta wadanda suka aiko tawaga zuwa wajensu.
A lokacinda suka tabbatar da cewa an ganosu, sai suka fita daga cikin kogon. Sai Rafa’ah dan Shaddad wanda ya kasance matasahi wanda yake ji da karfinsa ya haw dokinsa. Sannan ya fadawa Khuza’i kan cewa zai yakesu a madadinsa. Sai yace masa, ba abinda hakan zai amfaneshi, don haka yayi kokarin ya kubutar da kansa, idan zai iya.
A cikin wannan halin ne sai dan shaddad ya far masu ya kuma tarwatsasu, sun tsere. Sun yi kokari su kama amma suka kasa. Saboda ya kore a yaki da kibiya.
Amma shi shi Amru Alkhuzaei, bai da lafiya ba zai iya yin kome ba, saboda an shayar da shi guba a bayan. Don haka suka kamashi, suka shiga da shi gari.
Sannan sun yi kokarin ya fada masu shi waye ne, amma yaki. Idan sun matsa sai ya ce masu. Shi mutum wanda idan sun taba shi zasu yi nadama, idan sun kasheshi zasu kara yin nadama. Daga nan suka rasa abinda zasu yi da shi, sai suka aika da shi zuwa wajen walin Musil a lokacin mai suna Abdurrahman, sai Abdurrahman ya gane shi, ya kuma rubutawa Mu’awiya wasika dangane da shi.
Sai Mu’awiya ya mayar masa da amsa, inda yake cewa, wai ance, ya soki Khalifa Ustham da kan kibiyarsa har sau 9, don haka a sokeshi shima sau 9.
Daga nan Abdurrahman ya sa aka fito da shi daga inda suke tsare da shi. Suka soke shi da kibiya mai kaifi har sau 9. Ance a suka ta farko ko ta biyu amru yayi shahada.
Sannan suka yanke kansa suka aikawa Mu’awiya wanda ya sa aka yi ta yawo da kan a cikin sham, a matsayin sakamakon wanda ya ke da hannu wajen kashe Khalifa Uthman. Sannan suka aikawa matarsa Amina, wacce take tsare a gidan yari a sham a lokacin, kan nasa. Inda ta yi kuka kamar zata mutu. Sannan ta ce a mayarwa Mu’awiya kan tare da fada masa wasu bakaken maganganu. A lokacinda yaji abinda ta fada sai yayi fushi ya sa aka zo da ita. Ba tare da wani tsoro ba ta cewa Mu’awiya ita ta zage shi.
Suka da musayar magangannu. Wasu sun ce masa ya kashe ta, amma ya ki, sai kawai ya ce mata ta bar sham kada ta sake dawowa. A nan ma ta ci gaba da maganganu mafu fusata mu’awiya har ta bar wurin.
Sannan mun kawo yanda Ziyad dan Sumayya ya sa a kawo masa Awfi dan Hisen wanda yake sukan siyasar Banu Umayya, sai ya boye daga baya, ya cewa kawo ya zo fadar sa daga nan ya gano Awfi, ya kuma kasheshi.
Wadan nan duk suna daga cikin sahabban manzon All..(s) wadanda Mu’awiya dan Abusufyan yasa aka kashe, saboda sonsu ga Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma iyalan gidansa tsarkaka.
Sai kuma Juwairiyya dan Mashar Al-Abdi, wanda ya kasance cikin salihan bayi, kuma yana daga cikin wadanda suka yi karatu a gaban amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a).
Wata rana sun hadu da shi, sai Imam (a) ya kira Juwairiyya, ya ce masa, mu hadu/ da suka hadu sai ya fada masu wasu daga cikin asiran iyalan gidan manzon All…(s). Daga ciki ya ce masa {Ya Juwairiyya! Kaso masoyimmu, matukar yana sommu, sannan ki ki makiyimmu matukar yana kimmu, idan ya somu ka so shi}.
Har’ila yau wata rana ya shigo wajen Amirul mumina (a) ya same shi yana kwance kamar zaiyi barci, sai yayi sallama, yana cewa (Ya kai mai barci, ka farka, Lallei san an daki kanka, duka wacce zata sa jininka ya jika gemunka, ).
Sai Imam Ali (a) ya yi murmushi, ya tashi, sai ya fada masa abinda zai faru da shi bayan shahadarsa, a hannun sarakunan banu Umayya. Yace: {Zan fada maka ya Juwairiyya dangane da Al-amrinka! Na rantse da wanda raina yake hannunsa, Lalle za’a zo da kai a gaban, ma’abucin mummunan halaye kuma shege, lallai sai ya yanka hannunka da kafarka, kuma lalle sai ya tsireka a kan kututture guntu}. Bayan shahadar Amirul muminina Aliyu dan Abu Talib (a), wata rana dan Sumayya ya kira Juwairiyya ya yanke hannusa da kafarsa, ya kuma sa aka tsere jikinka a kan wata kututture , kamar yadda Amirul muminina (a) ya fada masa.
Hashim dan Muhammad dan Sa’ib ya wallafa littafi kan kissan shi Juwairiya, da Rasheedul Adiy ko Rasheedul Bala da kuma Maitham Attammar. Wanda yake son karin bayani ya nemi littafin.
Sai kuma Abdullahi dan Yahya Hadrami, daya daga cikin wadanda suka kasance shi’ar Amirul muminina (a) na gaskiya, ya sha karatu mai yawa a wajensa. Sannan yana daga cikin Shurdatul Khamis.
Shurdatul Khamis sune wata Jama’a ko kuma jami’an tsaro wadanda Imam Aliyu dan Abitalib (a) bayan ya karbi shugabancin Al-ummar musulmi, bayan kissan Khalifa na uku Uthman bin Affan, ya kafasu. Ya kuma kulla al-kawali da su kan cewa ba zasu saba masa ba, a duk umurnin da ya basu. Shi kuma yayi masu alkawi kan cewa ya lamunce masu shiga aljanna a ranar kiyama.
Don haka a lokacinda aka kashe Amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a) sai Abdurrahman Al-hadrami ya ji zafi, ya kuma yi bakin ciki mai yawa. Sai aka gina masa wani wuri don bauta a wajen Kufa. Don haka da shi da wasu muminai tare da shi suka koma wurin suna bautar All..T. bayan da Mu’awiya ya karbi shugabancin al-ummar Musulmi ya bada umurni a zo masa da su. Aka zo da su sai ya bada umurni a kashesu gaba daya.
Wadannan da muka ambata, salihan bayi ne daga cikin musulmi. Wadanda suke son Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) matukar so, wanda babu karya a cikinsu. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, shudatul Khamis wanda wasu daga cikinsu suke ciki, sun kai matsayinda a cikin musulmi a lokacin idan sun bada shaida a duk inda ake bada shaida, ana karban shaidar mutum guda daga cikinsu ba tare da an nemo na biyu ba.
Mu’awiya dan Abu sufyan ya kashe wadannan bayin All..ba don kome ba sai don suna son waliyyin All..bawansa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Kuma sun so shi ne saboda bin umurnin manzon All..(s) na a so amirul muminina(a). Banda haka All..ya umurci musulmi su so iyalan gidansa, don sonsu shi ne ladan musulunci wanda Alll..T ya aiko shi da shi. All..yana cewa { ..Ka ce: “Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta.” Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya. } Ashura 23.
A hadisi an tambayi manzon All..(s) kan cewa su waye All..T yace a so su cikin danginka, sai yace Aliyu da fatima da yaynsu Al-Hassan da Al-Hussain (a). Don haka son Aliyu dan Abitalib (a) yana daga cikin ladan da All..T yace a bawa manzon All..(s) saboda aikarsa da isar da sakon addinin musulunci ga musulmi. Don haka sun aikata umurnin All..ne na son shi. Amma mu’awiya ya bisu daya bayan daya ya kashe su.
Banda haka mu’awiya bai takaita da kashesu kadai ba, yayiwa mabiya Amirul muminina (a) wasu karin laifuka inda ya bada umurni aka.
01-Rusa gidajensu. Mu’awiya dan Abu sufyan ya bai takaita da kashe shi’ar Amirulmumina (a) kadai ba, sai dai ya nada umurni a ruda gidajensu, a barsu ba tare da waurin zama ko tarewa ba. Wannan duk don shafesu daga doron kasa da kuma ganin ya kawo karshensu.
02-Rashin karban shaidarsu- Banda haka Mu’awiya dan Abusufyan, ya bada umurni ga gwamnoninsa kan cewa, kada su karbi shaidar shi’ar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib(a).
Shi ma wani mataki ne da ya dauka kan mabiya Ahlubaitin manzon All..(s), a kokarinsa na shafesu daga doron kasa. Don haka wadanda bai sami damar kashesu ba, ya takura masu, har ya kaskanta matsayinsu a cikin al-ummar musulmi, ya sa basu da kima hatta ta bada shaida na misali an ga watan azumi, ko don raba gardama tsakanin musulmi ko kuma bada shaida kan wani al-amari mai muhimmanci wanda ya faru a tarihin musulunci, kamar ruwaito hadisi daga manzon All..(s). Basu da wannan damar, saboda su ba amintattu bane a wajen Mu’awiya. Sannan ya san cewa idan ya basu wannan damar ba abinda zasu ruwaito ko su fada sai falalar mutuminsu. Wanda suka ji daga wajen manzon All..(s).
Da wannan dalilin ne, duk tare da cewa hadisi ya inganta daga wajen manzon All..(s) yana cewa {قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ صَلَّى اَللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ : أَنَا مَدِينَةُ اَلْعِلْمِ وَ عَلِيٌّ بَابُهَا فَمَنْ أَرَادَ اَلْمَدِينَةَ فَلْيَأْتِ اَلْبَابَ وَ قَالَ أَقْضَاكُمْ عَلِيٌّ . Ni birnin ilimine kuma Aliyu ne kofarsa, to duk wanda yake son shiga birnin ya zo masa ta kofarsa, ko kuma inda yace: {Aliyu ne mafi sanin hukunce hukunce daga cikinku} .
Amma a halin yansu da zaka nemi hadisan da aka ruwaito daga Amirulmumina A liyu dan Abitalib (a) zaka ba basu da yawa. Wasu malaman sun bayyana cewa, a cikin mazhabobin musulunci ko littafan hadisai hadisansa basu fi 50 ba ko kusa da hakan. Banda haka wasun ba karya aka masa. Don kaskanta shi.
Ta yaya za’a ce Abu Huraira wanda ya musulunci a shekara ta 7 bayan hijira, a shekarar yakin Khaibara, ya fi Aliyu (a) yawan hadisai a cikin musulmi. Inda suka ruwaito hadisi kimani 3000 daga wajnesa. Amma Aliyu wanda ya tashi a gidan manzon All..(s) shi ne ya koya masa cin abinci, an saukar da wahayi na farko yana tare da manzon All..(s) yana dan shekara 10 a duniya a lokacin amma ba’a ruwaito hadisan manzon All..(s) sai kimani 50?.
Wannan umurnin da mu’awiya dan Abu sufyan yayi na fasikantar da shi’arsa a cikin musulmi ne yana daga cikin alamura da suka sa babu hadisansa a ciki mafi yawan musulmi.