Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 220

220-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu dawarhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissashi wadanda suka zo

220-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu dawarhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissashi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu laiattafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da mukekawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka fara kawo maku, yanda Mu’awiya dan Abusufyan yasabawa sharadin sulhu na farko wanda Imam Al-Hassan (a) ya shardanta masa kafin ya mika masu shugabancin al-ummar musulmi.

Daga cikin mun fara da kada ya zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), sannan kada ya zutar da shiarsu, sannan ba basu hakkinsu, sannan ya bashi harajin dorobijar na kasar Farisa wadanda duk bai cika su ba.

Ya zagi Amirulmuminina (A) har ya maida shi sunna ya barwa na bayansa, sai da akalla aka yi shekaru 60 ana zaginsa a kan mimbarorin musulmi.

Ya ki ya bashi harajin dorabijar saboda kada yayi karfi ya kwace iko da hannunsa, ya kashe shiar Imam Ali da Imam Al-Hassan a duk inda ya samesu. Ya rusa gidajensu ya hana a basu hakkinsu da kudaden su. Ya sa ana wulakantasu a duk inda aka gansu. Mun yi maganar Kumait da kasidunsu kan yanda son Aliyu (a) ya zama musiba ga mabiyansa.

A yau zamu fara maganar Hijru dan Adiy wanda shi ma Mu’awiya dan Abusufyan da kansa ya bada umurni a kashe shi saboda yaki ya zagi Imam Ali (a).

Hijru babban sahabin manzon All..(s) ne wanda ya shahara da tsoron All..da kuma ibadansa, ana girmama shi a cikin sahabban manzon All..(s), saboda ibadarsa yana alwala a duk lokacinda ta warware sannan ya yi raka’o’i biyu. Kuma ana karban addu’arsa.

Daya daga cikin karamominsa shi ne a lokacinda aka kamashi aka tafi da shi zuwa sham, sai ya yi barci sannan ya yi mafarki ya bata kayansa, kuma baya son ya zauna da janaba, ya fadawa wanda yake kula da shi ya bashi ruwan da ke cikin kayansa yayi wanka da shi sai mutumin yaki.

Sai mutumin ya ki saboda yana jin tsoron Mu’awiya kada ya kashe shi idan ya bashi ruwa, sai Hijir ya ruki All..ya bashi hanya ya yi wanka,. sai aka ga gajumare ya zo yayi ruwan sama a inda suke da haka hijiru ya samu yayi wanda. Karaman Hijru yana da dama.

Amma Abinda ya hada shi da mu’awiya shi ne, bayan sulhunsa da Imam Alhassan (a) sai ya bawa ma’aikatansa umurnin su rika zagin Imam Ali(a) a kam mambarorin musulmi kamar yanda muka yi bayani a baya. A cikin wannan halin sai wata rana suna cikin mallaci a Kufa, sai walin Mu’awiya a Kufa Mughira Dan Shu’a ya tashi yayi Khuduba ya zagi Imam Ali(a). Hijru yana cikin masallacin, amma ya kasa hakuri, sai ya tashi ya fadawaMughari kan cewa wanda ya zaga din nan ya fi cancantar yabo, kuma wanda ya yaba kuma shi yi fi cancantar Zagi.

A lokacinda Mugira ya ji sai ya ce masa ni shugabanka ne me yasa kake magana a gabana kamar haka, sai wasu da dama daga cikin kabilarsa suka tashi suka tsaya kusa da shi suka sake fada abinda Hijiru ya fada. Sai mughara ya ce masa ya kai Hijiru ka ji tsoron fushin sarki, don in yayi fushi zai nika irinka irinka, ….yayi maganganu da yawa.

Amma hijiru bai sauya ba, yana bayyana kiyayyarsa ga shugabancin umayyawa, har sai da wasu fadawansa da suka bashi shawarar ya kashe shi, amma ya ki amsa kiransa, saboda kamar yadda y ace, bayason ya zama shi ne mai kisan manya manyan garinKufa.

Ko ba kome, Hijru dan Adiy sahabin manzon All..(s) sannan kowa ya san matsayinsa a matsayin shugaban kabilansa kinda. Ya yi aiki da Imam Ali (a) a matsayin Khalifa, sannan ya yi aiki da Imam Alhassan na tsawon watannin da yayi kafin ya mikawa Mu’awiya shugabancin.

Al-amarin Hijiru dan Adiy ya rikicewa Mugira walin Mu’awiya a Kufa, ya san cewa idan ya fara kissan mutanen Kufa to ya kama hanyar halaka ne kuma zai tabe a lahira, zai yiwa Mu’awiya aiki ya kyautata mulkinsa da duniyarsa, shi kuma ya tabe a Lahira don ya san in kashe Hijir ya kashe bawan All..kuma sahabin manzon All..(s).  

Mugira yaki ya dauki mataki a kansa, har mutuwa ta zo masa, sai fadawansa suka ce masa ya kashe Hijru, sai ya ce masu, zan mutu wani zai maye gurbi ne kuma shi ne kashe shi mafi sharrin kisa. Haka kuma aka yi ! Mugira ya mutu sai Mu’awiya ya aiko sabon wali zuwa kufa kuma shi ne Ziyad dan Sumayya, wanda kowa ya sanshi da sharrinsa,

Don haka Hijru ya ci gaba da nuna halayensa na kin irin salon sarauta na Banu Umayya, har zuwa wata rana Ziyad ya haw kan mimbari yana khudubar sallar Jumma’a. Ya tsawaita khudubar har lokaci zai fita, sai Hijru ya tashi yana masa inkarin abinda yake yi har zuwa lokacin sallar zai fita.

Amma ziyada ya ci gaba da Khudubarsa, sai Hijir ya sake daga mursa yana cewa Assalat, ziyad yaki ya kula da shi. Sai da suka ga lokaci zai fita sai hijira ya buga hannunsa a kasa yana cewa assalat duk mutane a masallacin suka tashi tare da shi suna fada. A nan ne sai ziyad ya sauka ya bada sallar jumma’a kafin lokacin ya fita.

Amma bayan haka Ziyar ya daukarwa kansa sai yi maganin Hijru. Ta yanda zai zama darasi ga sauran mutanen irinsa a Kufa. A wani wuri yana cewa (Ni ba kome bane, idan ban hana Hijru filin zama a kufa ba, kuma na sanya shi abin lura ga wanda zai zo bayansa ba. Bone ya tabbata ga mahaifiyar Hijir) sai yace  ya hijru:

Sai ya rera wata kasida wacce ma’anata na nuna cewa: garin gyaran gera sai aka rasa ido.

Da farko ziyad ya kira wasu manya manyan kufa mutanen kufa ya kuma umurcesu da su dawo da Hijr daga halayensa da kuma yanda yake mu’amala da shi. Amma sun yi kokari Hijr ya dawo daga halayensa ya ki amincewa. Daga karshe ya bukaci yansandansa su kama masa shi, su kawo.

Yansanda sun je kama shi amma sun yi ta buge buge da mutanen Hijr, daga karshe sun kasa kama shi.akwai wasu da dama daga cikin muminai da kuma danginsa wadanda suka hana a kama shi.

Daga nan sai Ziyad ya tara wasu manya manyan kabilun kufa, ya ce masu, ya ku mutanen kufa, shi zaku yi mani biyayya da hannu guda sannan ku saba mani da dayan hannun ne? Ko kuma a zahiri kuna tare da ni, amma hankalinku da sonku gaba daya yana wajen Hijr ne?.

Wawa ne kawai zai yarda cewa, kuna tare da ni, amma gaskiya shi ne, da ku da yayanku da danginku gaba daya, kuna tare da Hijr. Wannan kuma shi ne kha’incinku gare ni. Na rantse da All..ko ku bayyana mani kubutarku ko kuma in kawo maku wasu mutane wadanda zasu maidaku kan hanya.

Sai kawai suka fara tashi suna bayyana masa cewa suna tare da shi, kuma sun yarda da shugabancinsa. Sun rantse da All..kan cewa, bayyana cewa su basa da tare da wani sai shi da kuma biyayya ga amirulmuminina suna nufin mu’awiya. Ba abinda suke nema sai yardarsa.

Daga sai yace masu idan gaskiya ne, to ko wanne daga cikunku ya je tare da yayansa da makusantansa da kuma da duk wadanda suke biyayya gareshi ya raba Hijir da wadan nan mutane wadanda wadanda suke biyayya gareshi don musamu mu kama shi.

Daga nan sai wadan nan manya manyan mutanen kuma suka tashi suka batawa Hijir al-amarinsa, suka raba shi da wadanda suke kare shi daga jami’an tsaron ziyad. Suka bawa jami’an tsaro Ziyad damar kama shi da kuma jefashi cikin gidan yari.

Daga baya ya aiki shugaban jami’an tsaronsa Shaddaat dan Haitham Al-Hilali ya je ya kama Hijr amma ya kasa. Daga nan sai ya kira Muhammad dan Ashash al-kindi  ya ce masa: Ya baban Maitha, ko ka kawo mani Hijr ko kuma ba zan bar maka itacen dabino ba sai ya yankata, ko kuma gida sai na rusa shi, sannan sai na yayyakaka gunguwa gunduwa..

Sai muhammad yace masa, ka bani kwanaki uku zain gamsar da shi ya mika kansa. Sai yace: na baka, idan baka zo mani da shi ba ka dauki kanka matacce ne kawai.

Sai muhammad ya fita tare da shugaban yansandan Ziyad, suka yi ta fafatawa da masu goyon bayan Hijru sai da suka rabashi da masu goyon bayansa suka kuma kama shi suka kawo shi da makusantansa gaban Ziyad wanda ya bada umurni a jefa su cikin gidan kaso.

Daga nan sai Ziyad ya bukaci mutane su gabatar da mummunan shaida a kan Hijr da mutanensa, shaidu wadanda zasu bawa Mu’awiya damar kashe shi. Sai suka yi gabatar da shaidu. Wasu sunci, suna bin Aliyu(a), wasu suka ce suna aibata Uthman, wasu suka ce suna zagin Mu’awiya, amma Ziyad bai yarda da wannan shaida ba, sai yace: wannan duk bai wadatar ba.

A nan ne sai Abubarrata dan Abumusa Al-Ashari ya tashi ya rubuta wata shaida kamar haka. Ga nissansa.

(Wannan shi ne abinda Abubarrata dan Abumusa Al-Ashari ya shaida a gaban All..Ubangijin talikai, kan cewa Hijr dan Adiya ya daina biyayya ga shugabancin Mu’awiya ya kuma rabu da jama’a, ya la’ani Khalifa, ya kuma yi kira zuwa yakarsa, ya kuma tara wata jama’a yana kiransu zuwa kwance bai’a, ya kafirce da All..kafirce a bayyana.).

A nan ne Ziyad ya yarda da shahadar, ya kuma bukaci mustane su sanya hannnu su amince da shahadar, sai suka hadu suka bada shaida, shaida wanda ya kai akalla mutum 70. A lokacinda aka kaiwa Mu’awiya wannan wasikar sai ya bada umurni a kawo masa su damasq.  A kuma daure hannayensu da kafafuwansu da karfe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted