Saudia Da Masar Sun Bukaci Komawa Kan MoU Ta Islamabad

Kasashen Masar, Saudia, Pakistan, da Turkiya duk sun jaddada wajibcin komawa kan takardar fahintar juna tsakanin Iran da Amurka ta Islamabad don dawo da sulhu

Kasashen Masar, Saudia, Pakistan, da Turkiya duk sun jaddada wajibcin komawa kan takardar fahintar juna tsakanin Iran da Amurka ta Islamabad don dawo da sulhu da zaman lafiya mai dorewa a yankin yammacin Asia.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wadannan kasashe na fadar haka a yau Talata, a wani bayanin hadin giwa da suka fiyar. Sun kuma kara da cewa hanyar diblomasiyya da tattaunawa ce kadai zasu kawo karshen rikicin yankin.

Labarin ya kara da  cewa wadan nan kasashen hudu, sun bukaci a mutunta hurumin kasar saudiya, da kuma darajar kasar, sannan suna bukatar a warware dukkan matsalolin da ke faruwa da ita ta hanyar tattaunawa.

Dangane da kasar Sudan kuma kasashen sun bayyana damuwarsu da abinda yake faruwa a kasar Sudan, suna adawa da duk abinda zai raba kasar ko ci gaba da kawo cikas a rayuwar mutane kasar. Daga sun kasashen sun kara jaddada cewa har yanzun matsalar Falasdinawa itace babbar matsala a cikin kasashen musulmi da larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted