Kasashe 77 Ne Na Duniya Suka Fice A Lokacin Jawabin Fira Ministan Isra’ila A Taron Majalisar Dinkin Duniya

Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa

Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya

Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito cewa: Bayan duba kasashen da suka kaurace wa jawabin, an gano cewa: “dukkan makwaftan Isra’ila hudu, baya ga Saudiyya” na daga cikin mutane 77 da suka kauracewa taron, lamarin da ya sa Netanyahu ya yi magana a wani zauren da ke kusa da babu kowa.

Sabanin haka jaridar yahudawa ta yabi wakilan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da suka ci gaba da zama a zauren taron inda suka saurari jawabin Netanyahu, duk kuwa da takun saka tsakanin bangarorin biyu dangane da yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma burin wasu mambobin kawancen Netanyahu na mamaye yammacin kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted