Haramcin safarar jiragen ruwa ya shafi gwamantin yahudawan sahayoniyya ce da masu goya mata baya kawai
Jamhuriyar Yemen ta sake sabunta wasikar ta zuwa ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, inda ta jaddada cewa; Matakin haramta zirga-zirgar jiragen ruwa ya shafi ‘yan sahayoniyya ne kawai ko kuma duk wani bangare da ke gudanar da hadin kai da su. Ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki cikakken alhakinta tare da daukar kwararan matakai don dakile wannan ta’addanci da ke faruwa a Gaza, da samar da agajin gaggawa, da kuma kare al’ummar Falasdinu.
Hakan na zuwa ne a cikin wata wasika da Jamal Amir, ministan harkokin wajen gwamnatin canji da sake gina kasar Yemen ya aike zuwa ga shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a wannan wata na Yulin shekara ta 2025, Asim Iftikhar Ahmed, da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.
Wasikar ta bayyana cewa: Alkawari na ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa ya shafi dukkan kasashe da hukumomi in ban da ‘yan sahayoniyya da kuma wadanda ke tallafa musu da kayan aiki, ko soja ko kuma na tattalin arziki da ke taimakawa kai tsaye ko a kaikaice ga zaluncin yahudawan sahayoniyya kan zirin Gaza.