Rahotanni sun bayyana cewa kasar Venuzuwela ta bukaci a gudanar da taron gaggawa na kwamitin tsaro na majalisar dinkin bayan harin da kasar Amurka ta kai kasar da sanyi safiyar yau Asabar wanda shuagaban Amurka Donald trump yayi ikirarin cewa ya sa an kama shugaban kasar Nicolas Maduro.
Ministan harkokin wajen kasar venuzuwela Yvan Gil ya fadi cewa Gwamnatin karakas ta bukaci kwamtin tsaro na majalisar dinkin duniya da ya kira zaman gaggawa don mayar da martani kan harin da Amurka ta kai kan kasar venzuwela
A cikin wata wasika da jakadan kasar venuzuwela a majalisar dinkin duniya Samuel moncada ya mikawa majalisar yayi tir da harin da Amurka takai inda ya bayyana shi a matsayin yakin mulkin mallaka kan kasarsa, Jakadan ya yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da yayi Allah wadai da wannan hari ya bukaci a dakatar da ayyukan soji nan take, sannan a dorawa Washington alhakin laifukan cin zarafi da aka yi wa kasar venuzuwela.