Kasar Rasha Ta Bayyana Cewa: Ba Ta San Makomar Sansanin Sojinta A Kasar Siriya Ba

Ministan harkokin wajen Rasha ya yi magana kan makomar sansanonin sojin Rasha a kasar Siriya Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa: Kasar

Ministan harkokin wajen Rasha ya yi magana kan makomar sansanonin sojin Rasha a kasar Siriya

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa: Kasar Rasha ba ta da masaniya kan matsayin sabbin mahukuntan Siriya kan yarjejeniyoyin da aka kulla na samuwar sansanonin sojin Rasha a kasar, kuma ba ta samu wata bukata daga Siriya dangane da hakan ba.

Lavrov ya kara da cewa: Siriya kasa ce mai cin gashin kanta, kuma tana da hakkin ci gaba da amincewa da yarjejeniya da aka cimma a baya ko kuma rusa su tsakanin kasar da kasashen waje, don haka Rasha ba ta da masaniya game da matsayin sabbin mahukuntan kasar kan ci gaba yarjejeniyar ko sake dubi kansu, sannan bangaren Rasha bai ce komai ba kan batun yarjejeniyar.

Ya kara da cewa: Ko shakka babu sauyin gwamnati da ya faru da kuma sauyin hakikanin abubuwa “a kasa” na iya samun bullar wasu canje-canje ciki har da batun kasancewar sojojin Rasha a Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments