A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar.
Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen sama marasa matuki samfurin Mq-9 daga Amurka.
Gabanin isarsa kasar ta Katar, shugaban kasar ta Amurka ya fara yada zango ne a kasar Saudiyya inda ya sami kyakkyawar tarba daga mahukuntanta, tare da kuma da kulla yarjejeniyar kasuwanci ta billiyoyin daloli.
Saudiyyar ta yi alkawalin zuba hannun hajri a can Amurka da kudaden da su ka kai dala biliyan 500 zuwa biliyan 600. Haka nan kuma za ta sayi makamai na wasu biliyoyin daliloli daga Amurka.
Ita kuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da a yau ne shugaban kasar ta Amurka yake Ziyara a can, ta yi alkawalin zuba hannun jarin da ya kai dala tiriliyan daya a Amurkan a cikin shekaru 10.