Iran Ta Yi Watsi Da Shirin Amurka Na Dakatar Da Bude Wuta A Yakin Zirin Gaza Na Falasdinu

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da duk wata shawarar shugaban kasar Amurka game da tsagaita bude wuta a Zirin Gaza Mukaddashin ministan harkokin

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da duk wata shawarar shugaban kasar Amurka game da tsagaita bude wuta a Zirin Gaza

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran Ali Baqiri Kani ya yi watsi da shawarar Amurka dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar.

Baqiri Kani ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ziyarar da ya kai birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon a ranar Litinin da ta gabata yana mai bayyana cewa: Idan Amurkawa da gaske suke yi,  maimakon gabatar da tsare-tsare da sunan tsagaita bude wuta, to ya kamata ne su dauki mataki daya, wato dakatar da duk wani taimako da suke bai wa haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kani ya kara da cewa: Da zarar an daina taimakon gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, to lallai kayan aiki da karfin gwiwar aikata laifuka kan Falasdinawa zasu tsaya cak lamarin da zai tilasta kawo karshen yakin.

Dangane da yiwuwar barkewar rikici tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Baqiri Kani ya ce: Gwamnatin da ta kasa murkushe mayaka a Gaza, idan har tana da sauran hankali, bai kamata ta wurga kanta cikin rikici da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments