Kasar Iran Ta Yi Tofin Allah-Tsine Da Allah Wadai Kan Hare-Haren Sojojin Mamayart Isra’ila Kan Zirin Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan ci gaba da laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza Kakakin ma’aikatar harkokin

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan ci gaba da laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya yi ishara da karuwar laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke yi kan al’ummar Falastinu da kuma janyo shahadar Falasdinawa sama da 100 da ba su ji ba ba su gani ba a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ciki har da kisan gillar da aka yi wa dan majalisar dokokin Falasdinu Mohammed Faraj al-Ghoul da kuma shahararren malamin kur’ani na Falasdinawa Alaa Azzam da iyalansa. Ya yi la’akari da ci gaba da killace Gaza, wanda ya hada da hana abinci da magunguna da kuma kakaba yunwa da kishirwa ga mazauna yankin, tare da jefa bama-bamai kan tantuna da sansanonin ‘yan gudun hijira, wani mummunan laifin yaki da ake aikatawa a matsayin wani bangare na shirin ‘yan mulkin mallaka na kawar da Falasdinawa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah wadai da yadda gwamnatin Amurka da yahudawan sahayoniyya suke yin katsalandan da kuma yaudara na kafa cibiyoyi karkashin fakewar rarraba kayan agaji da mayar da su a matsayin tarko na kashe mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da kakaba masifar yunwa da kishirwa. Ya kuma jaddada alhakin da ya rataya a wuyan kowace gwamnati da kuma kungiyoyin kasa da kasa musamman wadanda suka shafi kare hakkin dan Adam da dokokin jin kai na daukar matakin dakatar da wadannan laifuka cikin gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted