Kasar Iran Ta Yi Maraba Da Gyara Batun Cewa; An Dakatar Da Jigilar Jiragenta Zuwa Kasar Lebanon

Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa

Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon

Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran, ba tare da batun soke jigilar jiragen saman Iran zuwa kasar Lebanon ba.

Gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma’a ya sanar da cewa: An yi watsi da furucin wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu da suka ce, gwamnatin Lebanon ta hana tafiyar jiragen saman Iran guda biyu zuwa kasar Lebanon da suke tashi a ranakun Alhamis da Juma’a, don haka ofishin jakadancin Iran a Lebanon ya bi sawun abin da ke faruwa, inda aka gyara matsalar ta hanyar tabbatar da izinin ci gaba da jigilar jiragen, tare da sanar da matafiya daga Iran zuwa Lebanon gudanar da tafiye-tafiyensu daga Iran zuwa Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments