Jakadan kasar Iran a MDD ya rubutawa babban sakataren MDD wasika inda yake maida martini kan tuhumar da kasashen Amurka, Burtania da faransa suke wa kasar, na cewa ita ta rikita yanking abas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Amir Saeed Iravani yana fadar haka a cikin wasikar ya kuma kara da cewa wadannan kasashen uku sun dauki wannan matakin a kan Iran ne don kauda hankalin duniya daga irin ta’asar da HKI take aikatawa a Gaza.
Kafin haka jakadun wadannan kasashe uku sun zargi kasar Iran da taimakawa kasar Yemen da makamai wadanda ta kai hare hare masu tsanane a tsakiyar birnin Tel aviv a makon da ya gabata.
Wadan nan kasashe dun bayyana haka ne ba tare da la’akari da irin ta’asan da HKI take aikatawa a gaza ba , inda akalla mutane 40,000 mafi yawansu mata suka rasa rayukansu. HKI tana samun makaman da take wannan kissan kiyashi ne daga wadannan kasashe uku da kuma wasu kasashen turai.
Labarin ya kara da cewa wasikar wacce ta isa hannun Antonio guterret a jiya Talata, har’iala yau ta isa hannuna shugaban kwamitin tsaro na majalisar.
Wasikar ta kara da cewa wadannan kasashe 3 sun yi shiru a kan dukkan ayyukan kissan mutanen da hki take yi a yankin.