Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Gwamnatin Amurka tana goyon bayan ta’addancin da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a fili kuma a wani lamari mai ban takaici a idon duniya baki daya.
A daidai lokacin da ake gudanar da alhinin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa a duniya, wadda ta kasance a irin wannan rana ta yau 21 ga watan Agusta, kungiyar kare hakkin wadanda ta’addanci ta shafa ta shirya taron karo na takwas mai taken “Koyi Da Masu Hakuri” a yayin gudanar da taron alhinin da girmama su, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya gabatar da jawabin nasa.