Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Tana Ci Gaba Da Rage Hadin Kan Da Take Bai Wa Hukumar IAEA

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Tana cikin matakin rage irin hadin kan da take bai wa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Tana cikin matakin rage irin hadin kan da take bai wa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa: Ma’auni a gare su dangane da ayyukan makamashin nukiliya da kuma tsarin aikin hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, shi ne tsari da dabarun da Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta gabatar, yana mai fayyace cewa: A halin yanzu haka Iran tana kan matakin rage irin hadin kai da take bai wa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.

A cikin bayanin nasa a taron kwamitin manyan alkalai na hukumar ta IAEA da aka fara a ranar Litinin: Muhammad Islami ya jaddada cewa: Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta duniya tana gabatar da rahoto ayyukanta kan shirin makamashin nukiliyar Iran a duk tsawon watanni uku ga kwamitin manyan alkalan hukumar, sannan a duk watanni shida ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, shin rahoton ya yi daidai da ayyukan da Iran take gudanarwa ko kuma bai yi daidai ba a karkashin cikakken shirin hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA kuma wannan shi ne babban abin da rahoton ya fi mayar da hankali kansa, kuma wannan rahoton ya ƙunshi sassa biyu kan tsarin aikin haɗin gwiwa, sannan ɗayan ɓangaren kuma shi ne kan batun kariya da kare yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

Domin a karkashin dokar aikin, hakan zai sanya a cire takunkuman da aka kakaba kan Iran, sakamakon haka dole ne Iran ta mayar da martani idan har ɗayan ɓangaren bai yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsa ba, saboda haka Iran ta dauki matakin rage hadin kai da take bai wa hukumar ta IAEA.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments