Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta

A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga

A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta.

Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya  a yankunan da aka ce nan ne za a kafa Daular Falasdinawa.

 Haka nan kuma gwamnatin kasar ta Holland ta kira yi jakadan HKI a birnin Hauge domin gargadinsa akan yanayin da ake ciki a Gaza, da cewa babu yadda za a iya ci gaba da jurewa akansa, ko kare dalilin jefa yankin cikin wannan halin.”

Wannan matakin na kasar Holland ya zo ne gabanin wani taro da tarayyar turai za ta yi a yau Talata domin jingine aikin tare da HKI a fagen nazari da bincike na ilimi, saboda ta ki tsagaita wutar yaki a Gaza.

Tun da fari, Fira ministan  kasar Holland Dick Schoof ya wallafa a sharin X cewa;  A yayin taron da kasashen turai za su yi, Kasarsa za ta  yi  matsin lamba akan ganin an dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da HKI, haka nan kuma kakaba takunkumai akan shigar da kayanta na kasuwanci zuwa kasuwannin turai.

Fira ministan na kasar Holland ya ce, ya fada wa shugaban HKI Ishaq Herzog wannan matakin da suke son dauka ta hanyar tarayya turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments