Kasar Guinea Ta Tsare sojojin Sierra Leon 16 Akan Sabanin Iyaka

Sojojin kasar Guinea sun kama sojojin kasar Saliyo 16 bayan da su ka zarge su da tsallaka kan iyaka da daga tutar kasarsu a cikin

Sojojin kasar Guinea sun kama sojojin kasar Saliyo 16 bayan da su ka zarge su da tsallaka kan iyaka da daga tutar kasarsu a cikin Guinea.

A can birnin Freetown kuwa mahukunta sun ce sojojin na Saliyo sun daga tutar kasarsu ne a cikin wani yanki na kasar tasu, ba kutse su ka yi cikin kasar Guinea ba.

Ma’aikatar tsaron kasar Guinea ta ce, A ranar Lahadi  sojojin sun shiga gundumar Koudaye akan iyakar faranah ba tare da an ba su izini ba, sannan kuma su ka kafa wani  tanti da daga tutar kasarsu.”

Sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta Guinea ta ce, sojojin na Saliyo sun yi kutse da zurfin kilo mita 1.4 a cikin kasar da ba tasu ba, don haka an kwace dukkanin kayan da suke a tare da su, kuma tuni an bude bincike domin gano abinda yake faruwa.

Ita kuwa kasar saliyo ta bayyana cewa; Sojojin nata suna kafa wata wani zango ne da kayan aiki a kan iyaka ta  Kalieyere a gundumar gundunar Falaba, da kasar Saliyo ce.” Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa, sojojin suna cikin wannan aikin ne sojojin Guinea su ka tsallako kan iyaka zuwa inda sojojin nasu suke, su ka yi awon gaba dasu.

Sabanin kan iyaka a tsakanin kasashen biyu ya samo ne tun a 1992-2002 da aka yi yakin basasa. A wancan lokacin kasar Guinea ta aike da sojoji domin su taimaka wajen fada da ‘yan tawaye, to amma bayan kare yankin ba su janye ba, sun ci gaba da zama inda suke.

Tun daga wancan lokacin ne ake samun sabani a tsakanin kasashen biyu, musamman akan yankin Yenga mai arzikin Lu’u’lu’u.

Kasar ta Saliyo tana fadi tashi ta fuskar diplomasiyya domin ganin an sake mata sojojin nata da su ka hada da wani jami’i. Haka nan kuma kasar ta sanar da kungiyoyin yankin da su ka hada “Ecowas” da kuma kungiyar kasashen da suke a gabar ruwan “Mano River”

Ita kuwa kasar Guinea ta bakin babban hafsan hafsoshinta, kira ya yi wa sojojin kasar da su kasance ckin Shirin ko ta kwana domin kare hurumin kasar da iyakokinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted