kasar Ghana Ta Shigar Da Kara Kan Rikicin Iyakar Teku Tsakaninta Da  kasar Togo

Kasar Ghana ta sanar da shirinta na zuwa kotun kasa da kasa, don dai-daita dadadden rikicin iyakar teku tsakaninta da makwabciyarta Togo, bayan da suka

Kasar Ghana ta sanar da shirinta na zuwa kotun kasa da kasa, don dai-daita dadadden rikicin iyakar teku tsakaninta da makwabciyarta Togo, bayan da suka kasa cimma matsaya a tsakaninsu.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Felix Kwakye Ofosu shi ne ya sanar da matakin, inda ya ce Accra ta sanar da Lome cewa za ayi amfani da dokokin Majalisar dinkin duniya da suka shafi teku wajen shata musu iyaka. Ya ce sun dauki wannan matakin ne domin kare ruruwar rikici a tsakanin kasashen biyu da ke yammacin Afrika.

Wannan matakin dai ya yi kama da irin wanda Ghana ta dauka a baya kan Ivory Coast a shekara ta 2017, inda kotun kasa da kasa da ke sauraron shari’ar teku ta yanke  hukunci akai, lamarin da ya nuna yunkurin da Accra ke yi na tabbatar da iyakar tekunta wanda ke da mahimmanci ga bangaren tattalin arzikinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted