A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%.
A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi.
Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen kasashe a duniya karfi ba, su mamaye harkokin kasuwanci su manta da wasu kasashen mabutan a bay aba. Ministan yace idan Amurka ta ci gaba da wannan halin, al-amarin zai iya zama zaman dabbobi a daje ne.
Tun bayan da Donal Trump ya sake dawowa fadar White House a watan Jenerun da ya gabata, ya kudurin anniyar dorawa kawayen kasar a kan harkokin kasuwanci kudaden Fito, sannan ya so ya mamaye kasashen Greenland, Canada, Panama da Mixico saboda abinda ya kira tsaron kasar Amurka.