Chadi Na Shirin Ficewa Daga Kotun ICC

7 kacal kotun ke tsare da su, kuma 6 daga cikinsu duka sun fito ne daga kasashen Afirka.Wannan babban mataki na Chadi ya zo ne

Gwamnatin Chadi ta yanke shawarar ficewa daga Kotun Manyan Laifuka ta Duniya ICC, bayan ta bayyana cewa kotun ba ta da amfani, ba ta adalci, kuma tana son takura wa kasashen Afirka ne ka wai.

Chadi ta bayyana cewa cikin bincike 13 da kotun ta ƙaddamar, guda 9 duka sun shafi Afirka ne, yayin da sauran 4 da aka bude a wasu yankunan duniya da ba su samu wani ci gaba ba.

Haka nan, ta bayyana cewa mutane 7 kacal kotun ke tsare da su, kuma 6 daga cikinsu duka sun fito ne daga kasashen Afirka.Wannan babban mataki na Chadi ya zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa ke zarginta da hannu a rikicin  da ke faruwa a makwabciyarta, wato Sudan, abin da ke ci gaba da daukar hankali musamman a fagen siyasar duniya.

Kasar Chadi ta dauki wannan matakin ne bayan kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar wadanda gwamnatocin soja ke mulka, suka sanar da ficewar su a watan Satumba

Ficewar daga ICC za ta ba wa shugabannin siyasa da na soji a Afirka kariya daga fuskantar shari’a a kotun Hague idan aka zarge su da take hakkin bil’adama. Ga kasar Chadi musamman,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted