Kasar Canada Ta Mayar Da Martani Akan Barazanar Donald Trump Na Mayar Da Ita Wata Jaha Ta Amurka

kasar Canada  ta bakin Fira Ministanta mai barin gado Justin Trudeau da kuma Ministar harkokin wajenta, Milani Juli ta ce ko kadan kasar ba za

kasar Canada  ta bakin Fira Ministanta mai barin gado Justin Trudeau da kuma Ministar harkokin wajenta, Milani Juli ta ce ko kadan kasar ba za ta taba mika kai ga barazanar da zababben shugaban kasar Amurka yake yi na shigar da ita a karkashin Amurka ba.

Zababben shugaban kasar ta Amurka Donald Trump wanda ya gabatar da jawabi a jiya Talata ya bayyana cewa mai yiyuwa ne Amurka ta kwace iko da kasar Canada, da mayar da ita jaha daga cikin jahohinta, tare da bayyana shugaban kasar Justin Trudeau a matsayin gwamna.

Donald Trump ya yi barazanar amfani da makamin tattalin arziki akan kasar ta Canada,wacce yace kaco-kau ta dogara ne da Amurka wajen ba ta kariya ta soja.

Fira ministan Canada Justin Trudeau ya kuma ce, ko kadan Canada ba za ta taba zama jaha a karkashin Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments