Ministan harkokin wajen kasar Canada Melanie Joly ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasarta a shirye take ta shiga yakin tattalin arziki mafi girma da gwamnatin zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Joly ta na fadar haka a birninWashington a ziyarar aiki da ta kai can a ranakun 15-17 na wannan watan da muke ciki.
A cikin mako mai zuwa ne zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump zai kama aiki a matsayin shugaban kasar Amurka na shekaru 4 masu zuwa, kuma a karo na biyu.
Trump dai ya bayyana cewa, idan ya kama aiki zai sanyawa kayakin kasuwanci wadanda ake shigo da su Amurka daga kasar Canada, kudaden fito na kashi 25%. Ya ce wannan shi ne tsarin tattalin arzikinsa a kan kasashen Canada, Mexico china da sauransu.
Joly ta kammala da cewa wannan shi ne yakin kasuwanci mafi girma tsakanin kasashen na arewacin Amurka. Sannan Amurka ce zata soma yakin.
Ta ce gwamnatin kasar a shirye take ta nuna turjiyya mafi koli a kan gwamnatin Trump, sannan kasar Canada na da matakai daban-daban da za ta dauka don tunkarar Amurka idan ta yi hakan.
Kasashen biyu dai suna da kan iyaka a tsakaninsu wanda ya kai kilomita 8,891, don haka mafi yawan kayakin kasar Canada da suke shigowa Amurka ta kasa ce.