A karon farko tun soma yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban bara, Isra’ila ta kashe wani kwamandan soji na kungiyar Falasdinawa ta Fatah a Lebanon.
Tun bayan da aka fara yakin Gaza a kullum ana musayar wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da sojojin Isra’ila, wadanda ke harin mayakan Hamas.
Amma a karon farko a jiya Laraba Isra’ila ta kashe wani dan kungiyar Fatah ta Falasdinu a wani hari da aka kai a kusa da garin Saida a kudancin kasar Lebanon.
A cewar Fatah da wata majiyar tsaron Lebanon, an kashe Khalil Al-Maqdah, ne a wani harin da aka kai kan motar sa a lokacin da yake kan tuki a kusa da sansanonin Falasdinawa da ke daura da Saida, babban birnin kudancin Lebanon.
Sojojin Isra’ila, a nasu bangaren, sun bayyana cewa sun kai hari kan wani “dan ta’adda” wanda ke safarar makamai a yammacin kogin Jordan”.
Shi ne karon farko da wanda aka kashe ya kasance dan jam’iyyar Fatah, jam’iyyar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas.
Reshen soja na Fatah ya yi Allah wadai da “kisan gillan”, a yayin da Mahmoud Abbas ya zargi Isra’ila da “rura wutar rikici a yankin”.