Karin Kneiss: Kasashen Turai Ne Suke  Taimakon Masu  Dauke Da Makamai Na Syria Da Kudi Da Muggan Kwayoyi

Tsohuwar ministar harkokin wajen kasar Austria Karin Kneiss ta bayyana cewa, kasashen na turai suna aikawa da makamai da muggan kwayoyi da kudade ga ‘yan-ina

Tsohuwar ministar harkokin wajen kasar Austria Karin Kneiss ta bayyana cewa, kasashen na turai suna aikawa da makamai da muggan kwayoyi da kudade ga ‘yan-ina da yaki a yammacin Asiya, domin su aiwatar da bakar manufarsu.

Tsahuwar minstar harkokin wajen ta kasar Austria ta rubuta a shafinta na “Telegram” cewa; Gwamnatocin kasashen turai suna aike wa makamai, muggan kwayoyi, kudade zuwa ga ‘yan ina-da yaki zuwa yankin yammacin Asiya da kewayenta.”

Karin Kneiss ta kuma bayyana cewa kamar yadda kasashen na turai suke aikewa da makamai da kudi da muggan kwayoyi zuwa Syria haka suke aikewa  da su zuwa kasar Ukiraniya.

Karin Kneiss ta kuma bayyana amincewa da abinda ta ce wani abokinta dan kasar Syria ya siffata ‘yan ta’adda da cewa; masu bakar aniya ce.”

Ta kuma nakalto abinda abokin nata ya bayyana na cewa, ‘yan ta’addar suna da makamai, jirage marasa matuki da kuma kwarewa da suke nuni da cewa sun same su ne daga kasashen turai, kuma su ne su ka ba su horo.

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Syria suna nuni da cewa, kungiyar nan ta “Tahriru-shsamn, tare da kungiyoyin ta’addanci da take kawance da su sun bude yaki gadan-gadan a bangarori mabanbanta na kasar Syria,musamman a Halab da Idlib.

 Ma’aikatar tsaron Syria ta sanar da cewa, tana  kan ganiyar dakile hare-haren na kungiyoyi masu dauke da makamai a kusa da Humah.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments