Search
Close this search box.

Kani: Iran Da Siriya Ginshikai Ne Na Tabbatar Da Zaman Lafiya Mai Dorewa A Yankin Asiya Ta Kudu

Ministan harkokin wajen  kasar Iran na wucin gadi Muhammad Bakiri Kani ya bayyana cewa kasashen Iran da Siriya ginshikai ne a kokarin samar da zaman

Ministan harkokin wajen  kasar Iran na wucin gadi Muhammad Bakiri Kani ya bayyana cewa kasashen Iran da Siriya ginshikai ne a kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa a gabas ta tsakiya, kuma zasu ci gaba da aiki tare don cimma wannan manufar.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Bakiri yana fadar haka a lokacinda yake jawabin hadin guiwa da tokwaransa na kasar Siriya faisal Maqdad a birnin Bamascus babban birnin kasar Siriya.

Ministan ya kara da cewa kasashen biyu sun yi aiki tare fiye shekaru 40 da suka gabata, kuma sun tabbatar da cewa HKI ce asashen rashin zaman lafiya a yankin.

Ya kuma kara da cewa kasashen biyu tare da kasar Iraki sun yi aiki tare don ganin bayan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a lasashen Siriya da Iraki.

A nasi bangaren Faisal Muiqdad ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bukaci ganin dangantaka tsakanin kasashen Iran da siriya a dukkan bangarori sun ci gaba kamar yadda suke ko ma fiye da haka , bayan shahadar marigajiyi ministan harkokin wajen na kasar Iran Dr Hussain Amir Abdullahiyan.

Wannan dai shi tafiya ta farko na mukaddashin ministan harkokin wajen kasar ta Iran tun bayan karbansa mukumin mukaddasgin ministan harkokin wajen a ranar 20 ga watan mayu da muke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments