Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya bayyana cewa; Wadanda suke daukar kansu a matsayin Magadan Alaxender the great’ za su fuskanci makokar valarin sarkin daukar Roma na rusunawa a gaban Iran.
Kalibaf wanda ya wallafa sako a shafinsa na sadarwa X; a jiya Juma’a ya mayar da martani ga ministan harkokin wajen Amukra wanda ya yi maganganu na wauta akan tarihin ci gaban al’ummar Iran yana mai ce masa:
” A tsawon tarihi, mu Iraniyawa mun yi gaba da gaba da mutanen da su ka dauki kawunansu a matsayin shugabannin duniya, su ka kuma yi kokarin shafe tsohon ci gaba dake doron kasa.:
Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce: Wadannan mutanen sun zo da muggan kayan yaki, amma a karshe su ka koma cikin kaskanci, kuma a wulakance.”
Muhammad Bakir Kalibaf ta kuma ce; Wadanda suke kokarin zama Magadan Alaxander za su fuskanci makoma irin ta sarki valerian na daular roma da ya rusuna agaban Iran.