Baqaei : Iran Ta fi fifita Tsaron ta kan Tattaunawa

Kakakkin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’il baqa’I ya bayyana cewa iran ba ta da wani shiri na komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka madama

Kakakkin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’il baqa’I ya bayyana cewa iran ba ta da wani shiri na komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka madama tana ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin kasashen biyu a watan da ya gabata.

Isma’ila baqa’I ya fadi a jiya laraba cewa iran a halin yanzu ta mayar da hankali wajen mayar da martani kan hare-haren da kasar Amurka take kawo Mata ne,  don haka babu  wani shiri na tataunawa da Amurka ,  kuma wannan yana mayar da martani kan ikirarin da shugaban Amurka Trump yayi ne na cewa za su ci gaba da kai wa iran hari har sai ta koma teburin tattaunawa

Iran ta yi watsi da zargin da Amurka ta yi mata tana cewa an bawa iran alhakin kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hurmuz, hanyar ruwan tekun fasha wadda ke da matukar muhimmanci ga samar da makamashi na duniya, karkashin sashe na 5 na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Tehran da Washington.

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da take kai hare-hare a yankunan dake bakin teku a kudancin iran wanda wahington take ikirarin cwa tana yi ne don raunata karfin ikon iran na kai hari kan jiragen ruwanta a mashigar Hurmuz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted