Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Fadadar ayyukan wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya zai share fagen fadadan ayyukan ta’addanci a kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Duk da saurin ci gaban al’amura a kasar Siriya, suna tuntubar dukkanin bangarorin da ke da alaka da kasar ta Siriya, yana mai gargadin cewa: Fadadawar wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya a kasar Siriya zai kara share fagen fadada ayyukan ta’addanci, don haka dole ne a kan dukkan kasashe su nuna damuwarsu kan halin da ake ciki a kasar Siriya.
Baqa’i ya jaddada cewa: Dole ne kasar Siriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya mai cin ‘yancin kanta, yana mai nuni da cewa; Yahudawan sahayoniyya sun mamaye yankuna da dama na kasar Siriya, kuma fadada kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Siriya zai share fagen fadada ayyukan ta’addanci, yana mai nuni da cewa ta’addanci cuta ce mai yaduwa da matsalarta ba ta tsayawa a wani kebantaccen iyaka, tana barazana ga dukkan ƙasashe.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta damu da harkokin tsaro kuma har yanzu tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a yankin.