Kakakin gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da harin da ‘yan mamaya suka kai kan cibiyoyin yada labarai a kasar Lebanon
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatima Mohajerani ta jaddada cewa: Harin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan cibiyoyin yada labarai a kasar Lebanon alama ce da take nuni kan babban bala’i, tana mai cewa: Masu aikata muggan laifuka a koda yaushe suna kokarin hana duniya sanin laifukan da suke aikatawa.
Malama Mohajerani ta ce: An samar da yarjejeniyar Geneva da kuma dokar kare rayukan ‘yan jarida a cikin yanayi na yaki ta yadda bude hanyoyin sadarwa za su hana boye aikata laifuka.
Kakakin gwamnatin kasar ta Iran ta yi nuni da cewa: Harbe-harbe da harin da ‘yan ta’addan yahudawan sahayoniyya suka yi kan cibiyar ‘yan jaridu na tashoshin Al-Mayadeen da Al-Manar ba kuskure ba ne, aikin ta’addanci ne kawai da ke neman boye wa duniya irin ta’asa da barnar da ‘yan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza da Lebanon.