Kafafen Watsa Labarun  HKI: Nasrullah Ya Cika Alkawalin Kai Wa Sabbin Wurare Hari

A karon farko dakarun kungiyar “Hizbullah” na kasar Lebanon sun kai hari akan sansanin sojan na “ Jabalu-Nirya”, haka nan kuma wasu sabbin cibiyoyi da

A karon farko dakarun kungiyar “Hizbullah” na kasar Lebanon sun kai hari akan sansanin sojan na “ Jabalu-Nirya”, haka nan kuma wasu sabbin cibiyoyi da sansanonin ‘yan mamaya.

Kafafen watsa labarun HKI sun  bayar da labarin abinda ya faru na karshe akan iyaka, inda su ka ambaci cewa; Shugaban kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah, ya cika alkawalin da ya yin a fadada fagen yakin.

Bugu da kari, kafafen watsa labarun HKI sun ce Hizbullah ta kai wasu hare-haren a garuruwan “Tosorail’ da “ Hur-Fish” wanda hakan fadada yankunan da wutar kungiyar take isa ne.

Ita kuwa tashar talbijin din: 13, ta bayar da labarin da yake cewa; Ya zama wajibi mu ambaci cewa, yanayin da ake ciki a Arewa yana da ban tsoro.”

A ranar 17 ga watan Yuli din nan ne dai Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa; Matukar HKI ta cigaba da kai hare-hare akan fararen hula, to kungiyar gwgawarmaya za ta harba makamai masu linzamai zuwa sabbin yankunan da a baya ba a kai wa hari ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments