Sojojin Iran sun sanar da cewa: Gobara ta tashi a kan jirgin ruwan mai bayan ya afka kan wata nakiyar ruwa a gabashin mashigar ruwan Hormuz
Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ta Iran ya sanar da cewa: Gobara ta tashi a kan wani jirgin ruwa mai ɗauke da mai da ke aiki a Gabashin Mashigar Hormuz bayan ya afka kan wata nakiyar ruwa.
Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ya bayyana cewa: Jirgin ruwan, wanda ke tafiya a safiyar yau a Gabashin Mashigar Hormuz, yayi watsi da gargaɗin da aka maimaita ya bi ta hanyar da aka hana bi kuma maras aminci, don haka ya wurga kansa cikin hatsari, sakamakon haka ya afka kan wata nakiyar ruwa lamarin da ya janyo tashin gobara kansa.
Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ya jaddada cewa wannan shine makomar dukkan jiragen ruwa da suka yi watsi da gargaɗin kuma suka yi tafiya a wuraren da aka haramta.
Iran