Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-Hare A Wasu Wurare A Kudancin Kasar Lebanon

A ci gaba da keta hurumin yarjeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hizbulla ta kasar Lebanon, jiragen yakin HKI sun kai hare hare–hare a wasu

A ci gaba da keta hurumin yarjeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hizbulla ta kasar Lebanon, jiragen yakin HKI sun kai hare hare–hare a wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon sannan jiragen sun yi shawagi a kan birnin Beirut babban binrnin kasar a jiya Jumma’a.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon (NNA) yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, jiragen yakin HKI a jiya Jumma’a sun yi shawagi kasa-kasa sosai a kan birnin Beirut babban birnin kasar, sannan sun kai hare-hare kan wasu gine-gine a yankin Nabatiyya na kudancin kasar.

Labarin ya kara da cewa jiragen yakin HKI sun yi shawagi a kan wasu yankunan kusa da kogin Litan a kudancin kasar.

NNA ya kammala da cewa tun bayan fara aiki da tsagaita budewa juna wuta tsakanin HKI da kasar Lebanon a ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, sojojin HKI sun keta hurumin tsagaita wutar har sau fiye da 60.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bayyana cewa a cikin hare-haren da HKI ta kai kan kasar Lebanon, bayan tsagaita wuta, mutane 14 ne suka yi shada a kasar a yayinda wasu 13 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments