Kafafen yada labarai na kasar Yemen sun bada labarin cewa jiragen yakin kasashen Amurka da kuma Burtania sun kai hare-hare a kan wasu wurare a birnin San’aa babban birnin kasar.
Tashar talabijin ta Al-Mayadeen mai watsa shirye-shiryensa da harshen larabci a kasar Lebanon ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Yemen na cewa, jiragen yakin Amurka da Burtaniya sun kai hare hare a kan lambun ranar 21 ga watan satumba da ke tsakiyar birnin San’aa babban birnin kasar.
Sannan tashar talabijin ta Al-Masirah ta gwamnatin kasar Yemen ta bada sanarwan cewa jiragen yaki na kasashen biyu sun kai hare hare a kan wurare 6 a birnin San’aa wanda ya hada da ma’aikatar tsaron kasar.
Labarain bai bada sanarwan irin asarorin rayuka da dukiyoyin da aka yi a wadannan hare hare ba.
Tun ranar 11 ga watan Jenerun shekara ta 2023 ne, bayan samu izinin kwamitin tsaro na MDD gwamnatocin kasashe Amurka ta Burtaniya suka fara kai hare haren kan kasar Yemen don dakatar da takunkumin da ta dorawa jiragen kasuwancin HKI ko masu zuwa HK wucewa ta taken Maliya ko kuma mashigar ruwa ta Babul Mandab dake bakin Maliyaekun Arabia.
Kasar Yemen dai ta ce ba zata dauke wadannan takunkuman da kuma hare-haren da take kai HKI ba , sai ta kawo karshen yakin fin karfin da takewa falasdinawa a Gaza.