Search
Close this search box.

Jiragen Saman Yakin Yahudawan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Falasdinawa

Hare-haren ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan garuruwan Khan Yunus, Rafah da sansanonin Nuseirat, Al-Maghazi da Jabaliya sun janyo shahadan Falasdinawa masu yawa Falasdinawa takwas ne suka

Hare-haren ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan garuruwan Khan Yunus, Rafah da sansanonin Nuseirat, Al-Maghazi da Jabaliya sun janyo shahadan Falasdinawa masu yawa

Falasdinawa takwas ne suka yi shahada a safiyar yau Juma’a tare da jikkantamasu yawa sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai musamman kan sansanonin ‘yan gudun hijiran Falasdinawa na Nuseirat da Al-Maghazi da Jabaliya baya ga garuruwan Khan Yunus da Rafah da suke kudancin Zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na “Wafa” ya nakalto daga majiyoyin kiwon lafiya na Falasdinu cewa: Wasu Falasdinawa 3 sun yi shahada tare da jikkata wasu bayan wani farmaki da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wani gida na iyalan Matar da ke yammacin sansanin Nuseirat a tsakiyar Zirin Gaza.

Haka nan wasu Falasdinawa biyu kuma sun yi shahada sakamakon wani hari makamancin haka da aka kai kan wasu gidaje a sansanin Maghazi da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments