Jiragen Saman Yakin Isra’ila Sun Yi Luguden Wuta Kan Yankunan Gaza

Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila da makaman atilarinsu suna ci gaba da kai hare-hare da kuma luguden wuta kan Gaza Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya

Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila da makaman atilarinsu suna ci gaba da kai hare-hare da kuma luguden wuta kan Gaza

Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 466 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kuma harba makaman atilari, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai a sakamakon killace yankin da suka yi don hana shigar da kayayyakin jin kai musamman ga ‘yan gudun hijiran Falasdinawa, baya ga kashi 95 cikin dari na al’ummar yankin da suka fice daga yankin domin tsira da rayuwarsu.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare da kuma luguden wuta a yau Talata kan sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suka auna kan gidaje, wuraren taruwar ‘yan gudun hijira da kuma kan tituna, lamarin da ke haddasa shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkatan wani adadi na daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments