Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan wasu garuruwan kudancin kasar Lebanon
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na “Wafa” ya watsa rahoton cewa: Jirgin saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila maras matuki ciki ya kaddamar da wasu hare-hare kan garin Hanawiyeh, inda daga cikin farmakin ya nufi kan wata motar fararen hula, ba tare da haddasa hasarar rayuka ba. Kamar yadda jiragen yakin sojin yahudawan sahayoniyya marasa matuka ciki suka yi luguden wuta kan garin Maroun-Ra’as, sannan jiragen saman yaki da na marasa matuka ciki suka yi shawagi a sararin samaniyar yankin kudancin kasar ta Lebanon.
Sannan bayan tsakar dare, jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka afkawa garuruwan Ramiya da Alma al-Sha’ab.