Kungiyar Jiahadul Islamani wacce ake saran zata mikawa HKI wasu daga cikin fursinonin yahudawa a safiyar yau, ta yi gargadi ga HKI kan cewa, ta yi hankali, don tana iya karban gawakin fursinonin, mai makon karbesu da rayukansu.
Tashar talebujan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar na fadar cewa, hare-hare masu tsanani wadanda jiragen yakin HKI suke kaiwa a cikin yan sa’o’i na karshem kafin a fara tsagaita wuta, su na iya zama sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin fursinonin da ake shirin mika su idan an jima.
Kungiyar ta Bukaci iyalan fursinonin su takurawa HKI kan wannan hatsarin da ke gaban yanuwansu.
Ana saran fursinoni 33 yahudawa da falasdinawa kimani 730 ne, za’a yi musayarsu. Da misalign karfe 8.30 a lokacin Gaza, daga cikinsu akwai fursinoni mata guda 3 a cikin wadanda za’a yi musayarsu.