Jihadul-Islami Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Gwagwarmaya Har Sai Falasdinawa Sun Samu ‘Yancinsu

Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan

Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa

Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza.

A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki.

Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka samar da su don ‘yantar da kasa da kuma yakar makiya, kuma ba za a karbe su ba har sai an cimma wadannan manufofi guda biyu.”

Dangane da farmakin ‘yan mamaya da ake kira “Gideon 2”, sanarwar ta jaddada cewa sakamakon wannan farmaki “zai fi zama abin takaici, wajen shan kashi, da kwasar kaskancin makiya ‘yan shayoniyya.”

Sanarwar ta ce Sarayal-Quds da sauran kungiyoyin gwagwarmaya, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen lalubo hanyar kawo karshen wannan yaki da kuma wahalhalun da al’ummar Zirin Gaza suke ciki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments