Wani masanin tattalin arziki dan kasar Amruka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa; A halin yanzu duniya tana shiga cikin wata matsalar tattalin arziki mai hatsari saboda halin da ake cikin a mashigar ruwan Hurmuz, wanda daya ne daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci da makamashi yake wuce wa a duniya. Haka nan kuma takin zamani, dangogin man fetur da kuma alminium duk suna wucewa ta wannan mashigar ruwan.
Sachs wanda yake Magana a yayin hirar da fitaccen dan jaridar nan na Amumra Tucker Carson ya yi da shi, ya ce; Sako komawa yaki da Iran zai iya zai iya jefa duniya cikin yanayi da ba za a iya shawo kansa ba, don haka ya zama wajibi a kaucewa komawa yaki.
Masanin tattalin arzikin dan kasar Amurka ya ce duk wani hari da za a kai wa Iran, to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani daga Iran akan cibiyoyi masu muhimmanci a cikin wannan yankin.