Wall Street Journal: Har Yanzu Isra’ila Na Neman Wajen Da Zata Tura Falasdinawa Gudun Hijira

Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran

Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran Falasdinawan Gaza!

Jaridar Wall Street Journal ta buga wani rahoto da ke cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da tattaunawar da ta bayyana na zaman natsuwa domin tura ‘yan gudun haijiran Falasdinawa daga Gaza. Kasashen da suka hada da Libiya, Siriya da Sudan ta Kudu.

Rahoton wanda Samar Sa’ed, Robbie Gramer, da Omar Abdel Baqi suka shirya, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suke yunkurin tura dubban daruruwan Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa gare su, matakin da suka gabatar cewa akwai hanyoyin jin kai, amma gwamnatocin yammacin Turai da kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da shi da cewa ba gaskiya ba ne, kuma abu ne ba mai yiwuwa ba sannan keta dokokin kasa da kasa ne.

Jaridar ta kara da cewa: Ra’ayin da jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila suka yanke lamari ne da ya bayyana a bainar jama’a tun farkon yakin Gaza kuma ya dauki hankula a farkon wannan shekarar lokacin da Shugaba Trump ya ce Amurka na son karbe ikon yankin tare da sake gina shi a matsayin wurin yawon bude ido na kasa da kasa, tare da mayar da da yawa daga cikin mazaunansa miliyan biyu matsuguni mai aminci.

Masana sun ce gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suna kuma matsa wa Masar lamba don karba tsugunar da al’ummar yankin zirin Gaza a Sinai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted