Janar Salami:  Iran Za Ta Yaye Kallabin Sabbin Biranen Karkashin Kasa Na Ajiyar Makamai Masu Linzami Da Jirage Marasa Matuki

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran din Janar Husaini Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin babbar taron kasa na masu

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran din Janar Husaini Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin babbar taron kasa na masu ziyarar wuraren yaki a Abadan ya ce; Al’ummar Iran suna son ganin kasarsu tana gudanar da ayyuka a cikin kowane fage da cikakken karfi da kuma cigaba.

Janar Salami ya ce, dakarun kare juyin musulunci suna gudanar da ayyukansu a bisa wannan ka’idar ta  cigaba da kuma karfi, kamar yadda al’ummar kasa suke so. Haka nan kuma ya ce, babu yadda za a samu nasara a cikin rauni, kuma komai yawan makaman da ake da su, to imani ne yake tabbatar da duga-dugai.

Kwamandan dakarukun kare juyin musuluncin na Iran ya yi watsi da abinda makiya suke riya cewa, sanadiyyar sauye-sauyen da suke faruwa a bayan nan a cikin wannan yankin, matsayar Iran ta samu koma baya,tare da cewa wannan shi ne abinda makiya suke ta fada da maimaitawa,yana mai tabbatar da jajurcewar kasar da kuma karuwar karfinta.

Janar Salami ya kara da cewa, karfin Iran ya kai ta yadda za ta mayar da martani akan abokan gaba daga cikin kasarta, ba tare da ta dogara da wasu daga waje ba, kamar yadda ya faru a yayin farmakin “Wa’addus’saduq 1-2”.

Kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Iran kasa ce mai karfi kuma muna mayar wa da makiya martani ne akan wannan ka’idar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments