Janar Safawi: Zaman Lafiyar Iran Na Tattare Da Yin Shirin Fuskantar Kowace Irin Barazana

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Manjo Janar Yahya Rahim Safavi, ya yi hasashen cewa za a iya sheda

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Manjo Janar Yahya Rahim Safavi, ya yi hasashen cewa za a iya sheda barkewar wani sabon yaki, kuma watakila bayan wannan yakin.

Safavi ya fada a cikin bayanan da kafafen yada labarai na Iran suka ruwaito cewa, Iran ba tana a cikin yanayi na tsagaita bude wuta ba ne, tana Kallon kanta ne a matsayin kasa da take cikin  wani yanayi na yaki, yana mai cewa duk wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta na iya rugujewa a kowane lokaci.

Ya kara da cewa, “Babu wata yarjejeniya da aka rubuta tsakaninmu da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, ko tsakaninmu da Amurka kan hakan.”

Mai ba da shawara kan harkokin soji ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa, Washington da Tel Aviv sun yi imanin cewa, ana samun zaman lafiya ne ta hanyar karfi  kawai, wanda ke tabbatar da cewa dole ne  Iran ta kasance mai karfi a yanki da ma duniya domin samun zaman lafiya.

Ya jaddada cewa “tsagaita bude wuta na nufin dakatar da yaki na wucin gadi, wanda za a iya komawa a kowane lokaci.”

Safavi ya kara da cewa, “Mu ma’aikatan soji muna kimanta  yanayi bisa ga mafi muninsa, da kuma yin Shirin tunkarar mafi munin yanayi.”

Ya yi nuni da cewa, wannan a lokaci guda ya hada da  diflomasiyya, kafofin watsa labarai, yanar gizo, makami mai linzami, da karfin soji na zahiri da kuma na boye, yana mai jaddada cewa “mafi kyawun tsarin tsaro shi ne shi ne zama cikin Shirin fuskantar duk abin da ake zaton zai iya faruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted