Birgediya Janar Naqdi wanda yake yin Ishara da barazanar Amurka akan amfani da makamin da ta kira; ” Uwar Bama-bamai” yana mai cewa a lokacin yakin kwanaki 12 Amurka ta yi amfani da bama-bamai masu nauyin ton 14, sai dai wasu daga cikinsu ba su fashe ba da hakan ya bai wa sojojin Iran damar tantance yadda yake da fahimtar yadda aka kera ta.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto Naqdi yana fadin cewa; Barazanar bayan nan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa Iran shi ne babban dalili akan cewa Amurkan ta ci kasa a gaban al’ummar Iran.
Haka nan kuma ya ce; Barazanar ta Amurka ba ta nuni da cewa ta sami nasara.
Bugu da kari, Muhammad Ridha Naqadi ya ce; A halin yanzu fasahar wannan makamin da yadda ake kera shi, yana a hannun Iran.
Har ila yau Naqadi ya yi bayani akan karfin makamai masu linzami da Iran take da su, tare da jan kunne da gargadi akan duk wani hari da za a kawo wa Iran,domin kuwa zai zama barazana ce ga harkokin zuba hannun jari da muhimman cibiyoyin da ake da su a cikin wannan yankin.
Jami’in na Iran ya kuma yi Ishara akan yadda al’ummar kasar suke fitowa a kowace rana ta Allah domin yin gangami da taruka da suke a matsayin Babbar katangar tsaro ta Iran.