Baki masu wakiltan kasashe fiye da 90 ne, wadanda suka hada da malaman addinin da wakilan wasu kungiyayi, har ila yau da wakilan gwamnatoci fiye da 30 ne zasu halarci gagarumin jana’iza ta shahid Jagora Imam Sayyid Aliyul Khaminaei wanda za’a fara a ranar jumma’a mai zuwa.
Labarin ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa na daya Mohammad Arafe ne yake jagorantar kwamitan har zuwa karshensa a nan kasar Iran da kuma Iraki.
Mai magana da yawun kwamitin Jana’izar ya bayyana cewa, an kammala dukkan shirye shirye na ganin an aiwatar da wannan rakiya na tarihi, a biranen Tehran Qom, Mashad da kuma Iraki cikin tsari da nutsuwa mai kyau.
Ali Akbar Poorjamshidian ya kara da cewa, karkashin babban kwamitin akwai kananan kwamitoci wadanda zasu kula da al-amura daban daban a cikin lokacin jana’izar. Tsarin yadda jana’izan zata kasance yana nan kamar yadda aka bayyana a baya.
A bangaren tsaro sojojin kasar zasu tsananta tsaron sama kasa da ruwa don tabbatar da an gudanar da al-amarin cikin zaman lafiya da nutsuwa. Ana saran yan jarida daga ciki da wajen kasar Iran kimani 300 ne zasu watsa yanda za’a gudanar da jana’izar.