Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu

Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku.

Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa  zai iya bugawa da shugaba Rajab Tayyib Urdugan a zabe mai zuwa.

‘Yan jam’iyyar ta adawa sun kada kuri’ar tsayar da Imam Ugulu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa, inda ya sami kuri’u miliyan 1.6 a tsakanin miliyan 1.7.

Shugaban jam’iyyar ta “National Party” Uzgur Uzil wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa an yi zabe na gwaji da miliyoyin mutane su ka zabi Imam a matsayin shugaban kasa.

Kasar Turkiya ta fada cikin dambaruwar siyasa ne bayan da aka kama ‘yan hamayyar siyasa kusan 100 da aka zarga da cin hanci da rashawa, da kuma taimakawa ta’addanci. Daga cikin wadanda aka kama da akwai Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin Istanbul.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments