Jam’iyyar Democrats Ta Kwace Iko Da Majalisun Dokokin Amurka

Jam’iyyar Democrats a Amurka ta lashe zaben majalisun dokokin kasar guda biyu, a zaben tsakiyar wa’adin da aka gudanar a jiya Talata. Wanda kuma ya

Jam’iyyar Democrats a Amurka ta lashe zaben majalisun dokokin kasar guda biyu, a zaben tsakiyar wa’adin da aka gudanar a jiya Talata. Wanda kuma ya bayyana a fili kan cewa masu zabe suka zarginsa da rashin iya harkokin gudanar da kasa kamar yadda ya dace.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, masana harkokin siyasa da dama sun danganta faduwar Jami’ar Repulican da al-amura da dama daga cikin, tsarinsa na dorawa kayakin da ake shigo da su daga kasashen waje kudaden fito, yakin da ya shiga a Iran ba tare da samun nadaraba. Da kuma munanan halayensa.

Tashar talabijan ta CNN ta bayyana cewa, democrats sun sami nasarar iko da dukkan Majalisun biyu a lokaci guda, wanda zai basu damar hana shugaban Trump wasu abubuwan da yake bukata a cikin shekaru biyu da suka rage masa.

Tace Democrats sun sami nasara a zaben sanates a jihohin South Carolina, Texas, Ohio, Kansas, da Iowa. Kuma texas bata taba zaben sanata Democrats bat un shekara 1994. Da kuma Kansas tun shekara 1932.

A cikin watanni 22 da yayi a fadar white house shugaba Trump yayi ta yin abinda ya ga dama saboda yana da goyon bayan jam’iyyar masu rinjaye a majalisar dattawa ko sanats. Kuma ba’a taba samun rinjayen jam’iyya guda mai rinjaye a majalisun biyu bat un shekaru kimani 50 da suka gabata.

Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, shugaban zai fuskanci matsaloli amma ba zai wahala sosai ba tunda yana da damar kin amincewa da wasu abubuwa wato Veto.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted