Kwamitin tsaro na yankin Kurdistan na kasar Iraki ya sanar da kama wani babban dan ta’adda na kusa da shugaban ISIS Abu Bakar Baghadadi
A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a jiya Juma’a ya ce: An kama dan ta’addan ne da ake kira da Saqrat Khalil, wanda aka fi sani da (Abdullah Al-Tafkheikhei), inda bayanai suka bayyana cewa mutum ne da ya kasance na kusa kuma amintaccen ga khalifan kungiyar ta’addanci ta ISIS.
A furucin da dan ta’addan ya yi ya bayyana cewa: Bayan ya shafe shekaru biyar a Turkiyya, ya koma Kurdistan na kasar Iraki dauke da fasfo na jabu, kuma nan take aka kama shi a cikin wani yanki da ke lardin.