Rahotannin da suke fitowa daga Najeriya sun ambaci cewa jami’an tsaron kasar su 7 sun bace a yankin arewa maso tsakiya, bayan da aka kai wa ayarinsu hari.
Jami’an tsaron da sun kai 80 suna aikin bayar da kariya ne ga masu aikin gyaran wuta, yayin da ‘yan bokoharam 200 su ka yi musu konton bauna a kusa madatsar ruwa ta Shiroro a ranar Litinin din da ta gabata,kamar yadda kakakin jami’an tsaron Babawale Afolabi ya bayyana.Sai dai ya ce an kashe maharan 50. Ana zargin kungiyar ta Bokoharam da yi wa wutar lantarkin kasar kafar angulu,inda a watan da ya gabata arewacin kasar ya zauna cikin duhun rashin wuta na tsawon mako daya bayan da masu dauke da bindigar su ka lalata injinan dake bayar da wutar.
Tare da cewa kungiyar ta Bokoharam tana gudanar da ayyukanta na ta’addanci ne a yankin Arewa maso gabashin kasar, sai dai mahukuntan kasar sun ce a halin yanzu kungiyar tana da samuwa a cikin yankin arewa maso tsakiya, musamman a jihar Naija.
A cikin watan Satumba da ya gabata kungiyar ta bokoharam ta kashe mutane 100 a yayinda su ka bude wuta akan mutanen dake cin kasuwa da kuma masu ibada, wasu kuma a cikin gidajensu.